Al’ummar Amurka suna kada kuri’ar zaben shugaban kasa karo na 47, inda ake karawa a tsakanin Donald Trump na jam’iyyar Republican da kuma Kamala Haris ta jam’iyyar Democrat mai mulki.
Tun da misalin karfe 6: 00 na safiya a agogon gabashin kasar ne aka fara jefa kuri’a. Da akwai wasu mutanen da su ka kai miliyan 80 da tuni sun kada kuri’unsu ta hanyar akewa da su da gidan waya.
A bisa al’ada tun daga 1960 ana fara kada kuri’ar ne a wani karamin gari mai suna; Dixville” dake jahar New Hampshire akan iyaka da Canada.
Adadin mutanen wannan kauyen bai wuce 100 ba, kuma a bisa dokokin Amurka, ana fara kada kuri’a ne da tsakar dare, sannan idan an gama, a rufe mazabun da suke cikinta.
Zaben na wannan shekarar yana cike da zaman fargaba a Amurka, bisa la’akari da abinda ya faru a zaben 2020. A wancan lokacin dai shugaba Donald Trump ya ki amincewa da sakamakon zaben bayan da ya yi zargin cewa an tafka magudi. Tashe-tashen hankula sun biyo baya ta yadda magoya bayansa su ka kutsa cikin ginin majalisar kasar, da hakan ya jawo masa suka da kuma bude shari’a a kansa.
Saboda tsoron afkuwar rikici irin wancan, gwmanatin Amurka ta kashe dala miliyan 55 domin daukar matakan tsaro da su ka hada da killace fadar mulkin kasar ta “White House” da katangar karfe. Haka nan kuma an baza jami’an tsaro a cikin muhimman wurare a cikin birare da dama.
Kuri’ar sauraron ra’ayin jama’ar kasar da cibiyoyi mabanbanta su kka gudanar tana nuni da cewa manyan ‘yan takarar biyu suna tafiya kafada da kafada da tazara kadan a tsakaninsu.