Ana maraba da Yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Lebanon da Isra’ila

Al’ummar yankin Gabas ta Tsakiya suna maraba da dakatar da ayyukan  ta’addanci kan kasar Lebanon da kuma bukatar dakatar da su a kan Gaza Al’ummun

Al’ummar yankin Gabas ta Tsakiya suna maraba da dakatar da ayyukan  ta’addanci kan kasar Lebanon da kuma bukatar dakatar da su a kan Gaza

Al’ummun kasashen Masar, Iran, Turkiyya, Lebanon da Jordan sun yi maraba da cimma yarjejeniyar dakatar da kai hare-haren wuce gona da irin haramtacciyar kasar Isra’ila kan kasar Lebanon, suna fatan hanzarta cimma irin wannan yarjejeniya kan Falasdinu.

Gwamnatin Masar ta bayyana yarjejeniyar a matsayin wani mataki da zai taimaka wajen fara matakin rage ta’addanci a yankin Gabas ta Tsakiya gaba daya, ta hanyar aiwatar da cikakken kuduri mai lamba 1701 na kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da dukkan bangarorinsa da kuma baiwa sojojin Lebanon damar girke sansaninsu a kudancin Lebanon.

Masar ta jaddada cewa: Yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma a kasar Labanon dole ne ta zama wani share fage na dakatar da hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke kai wa Zirin Gaza, yayin da ake kokarin kawo agajin jin kai ba tare da cikas ba bisa la’akari da munanan yanayi na jin kai a yankin, tare da dakatar da keta haddin da bai dace ba a cikin yankunan Falasdinawa da suke gabar yammacin kogin Jordan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments