Ana Cigaba Da Korar Sojojin Faransa Daga Nahiyar Afirka

Kasar Chadi wacce tana cikin masu dasawa da Faransan ta sanar da kawo karshen sansanonin sojan Paris a cikin kasar. Shima shugaban kasar Senegal da

Kasar Chadi wacce tana cikin masu dasawa da Faransan ta sanar da kawo karshen sansanonin sojan Paris a cikin kasar.

Shima shugaban kasar Senegal da jaridar “ Le Monde” ta yi hira da shi, ya bayyana cewa, a fili yake nan da wani lokaci kadan sojojin Faransa za su bar kasarsa.

Shugaba Bassirou Doomaye ya ce; Saboda kawai Faransa  ta dade a cikin kasar Senegal tun lokacin cinikin bayi, baya nufin cewa za ta cigaba da zama a cikin kasar.

Wannan matakin na kasashen Afirka dai yana zuwa ne a lokacin da Faransan take sake tunanin yadda za ta sauya salon zamanta a cikin nahiyar ta Afirka.

A baya dai kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar sun raba hannun riga da Faransa din ta kawo kawo karshen zaman sojojinta da ma tasiirnta na tattalin arziki a cikin wadannan kasashen.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments