Rahotanni da suke fitowa daga kasar Syria sun ce, ana ci gaba da yi wa daidaikun mutane kisan gilla a sassan kasar mabanbanta.
A kusa da garin Hamah, an kashe mutane 7 a bayana nan, bayan da wasu masu dauke da makamai su ka shiga cikin garin Tal-Zahab. Masu dauke da bindigar sun kutsa gidan fararen hula tare da bude wuta a kansu. Haka nan kuma maharan sun yi sata a cikin gidajen da su ka shiga.
An gano gawawwakin mutane 7 a cikin wadannan gidajen bayan ficewar maharan. An harbi mutanan ne dai a kai da hakan ya yi sanadiyyar rasuwarsu.
Kamfanin dillancin larabdun “Sputnik” ya nakalto cewa, masu dauke da makaman sun kuma kame mutane da dama daga cikin wanann garin, tare da tafiyar da su zuwa wani wuri da ba a san ko ina ne.
Da akwai tsoron cewa za a kashe wadannan mutanen da aka kama.
Wanann dai ba shi ne karon farko ba da ake yi wa fararen hula kisan gilla saboda banbancin akidarsu.
A bayan nan an kashe Dr. Hassan Ibrahim wanda yana daya daga cikin muhimman masu nazari da bincike a fagen ilimin kimiyya na kasar Syria, an kuwa tsinci gawarsa ne a garin “Ma’ariba” dake bayan birnin Damascus a ranar Asabar din da ta gabata. An kuma ga alamun azabtarwa kafin a kashe shi a sassan jikin nashi.