A jiya Alhamis ne dai majami’ar Roman Katolika ta sanar da zabar Robert Farncis wanda ya zabi sunan Leo 14,a matsayin shugabanta.
Zabar Robert Francis a matsayin Paparoma na 267 ya zo ne bayan kwanabi 2 da manyan malaman addinin majami’ar Roman katolika su ka dauka suna yin zaben.
A bisa al’adar majalisar, farin hayaki yana fitowa daga saman majami’ar da yake nuni da cewa an zabi sabon Paparoman, da hakan ya sa a ka rika kada karaurawa a cikin maja’mi’un birnin Roma.
Sabon Paparoman dan shekaru 69 ya zabarwa kansa sunan Leo 14 domin sake dawo da aiki da kyawawan halaye a cikin harkokin tafiyar da majami’ar kamar yadda Leo na farko ya yi a 1878 zuwa 1903.