An gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga al’ummar Falasdinu a sassa daban-daban na duniya, a yayin zagayowar cika shekaru 77 da ranar ‘’Nakba’’ cewa da masifa.
A Faransa da Ingila duk an gudanar da wannan zanga zanga a wasu sassan kasar.
A cikin jerin gwanon, an daga allunan da ke dauke da sakonni irin su “Falasdinu za ta rayu!” » ko “Dakatar da kisan kiyashi a Gaza”.
“Nakba ba wani lamari ne da ya faru a baya ba, yana ci gaba da faruwa ta hanyar korar jama’a, da amfani da bama-bamai,” kan al’ummar Gaza.
Masu zanga-zangar sun yi Allah wadai da tabarbarewar al’amuran jin kai a zirin Gaza tun bayan barkewar yakin kisan kiyashi da Isra’ila ta kaddamar a watan Oktoban 2023 bayan harin ba-zata da Hamas ta kai.
Masu zanga zangar dake dauke da tutocin Falasdinu a Paris, sun zargi hukumomin Faransa, da yin hadin gwiwa da Isra’ila ta hanyar yin gum da bakinsu.”
A Zirin Gaza tun daga ranar 18 ga watan Maris din 2025, lokacin da gwamnatin Sahayoniya ta ci gaba da kai hare-hare, tare da karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Hamas da ta fara aiki a ranar 19 ga watan Janairu, an kashe Falasdinawa sama da 3,000, lamarin da ya kawo adadin wadanda suka mutu a Gaza tun farkon yakin zuwa akalla mutane 53,272, galibi mata da kananan yara, sannan Fiye da mutane 120,673 kuma sun jikkata.