An Yi Kira A Bai Wa ‘Yan Hijira Saboda Sauyin Muhalli Kariya

Kungiyar kasa da kasa mai kula da ‘yan hijira ( IOM) tana yin kira ga shugabannin kasashen duniya da su bayar da kariya da kare

Kungiyar kasa da kasa mai kula da ‘yan hijira ( IOM) tana yin kira ga shugabannin kasashen duniya da su bayar da kariya da kare hakkokin wadanda suke rayuwa a yankunan da suke fama da matsalar sauyin yanayi.

A taron da ake yi a yanzu haka a  garin Belem na kasar Brazil kungiyoyi masu zama kansu dake fafutuka da rajin kare muhalli suna gabatar da shawarwari akan yadda za fuskacin matsalolin da duniya take fuskanta.

Kiran kungiyar ya ambato mutanen da sauyin yanayi ya tilasta musu yin hijira, ‘yan asalin kasa a cikin karkara da ‘yan gargajiya.

Ibtila’oin dabi’a irin su ambaliyar ruwa, zafi mai tsanani, fari da mahaukaciyar guguwa, suna tilastawa miliyoyin mutane barin gidajensu a kowace shekara. Da akwai da dama da ba su iya tsallake iyakokin kasashensu, suna ci gaba da zama a wasu yankuna nesa da gidajensu.

Kungiyar tana son ganin an taimakawa wadannan bangarorin na mutane a karkashin kare muhalli.

Masana suna bayyana cewa a nan gaba, za a sami wasu kasashen da za su nitse a karkashin tekuna da suke kara cikowa,ko kuma su zama wuraren da ba za za iya rayuwa a cikinsu ba.

Mataimakin Babbar darakta na kungiyar ( IOM), Ughoci Daniels ya bayyana cewa, samar da tsarin yin gargadin gaggawa, da ayyukan hidima a cikin yankunan da aka fi fuskantar hatsari, yana da matukar muhimmanci domin karfafa mutane su ci gaba da rayuwa a inda suke.

Daniels ya kuma ce; Da dama daga cikin wadanda su ka fice daga cikin muhallinsu saboda sauyin yanayi, suna fadin cewa sun fiifta komawa zuwa gidajensu. Sai dai kuma garuruwan nasu sun tashi daga yadda su ka san su a baya saboda sauyin yanaki. A dalilin haka, abinda ake da bukatuwa da shi, shi ne samar da abubuwan da za su karfafa su.”

A dalilin haka, Daniel ya yi fatan ganin taron da ake yi na kasar Brazil akan muhalli ya zama wanda zai daura dan Ba, a fagen samar da sauyi da kuma biyan asarar da aka samu saboda sauyin yanayin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments