An yi gangami a fadin duniya domin nuna goyan baya ga al’ummar Falasdinu a daidai lokacin da aka gudanar da bikin ranar Falasdinu a ranar 29 ga watan Nuwamba da MDD ta kebe.
A faransa a gudanar da irin wannan gangamin, inda suka yi Allah wadai da mamayar da gwamnatin Isra’ila ta yi wa Gaza da Yammacin Kogin Jordan, tare da bayyana goyon bayansu ga adawar Falasdinu.
Baya ga Faransa, Birtaniya, Jordan, Kuwait, Slovenia, Sweden, da Morocco an shirya zanga-zangar goyon bayan Falasdinu.
Masu zanga-zangar sun yi Allah wadai da mamayar Isra’ila, ayyukan matsugunan Yahudawa a Yammacin Kogin Jordan, korarsu, da kuma kisan kiyashin Falasdinawa a Gaza da kuma cin zarafin fararen hula.
Daga cikin taken da aka yi da kuma rubuce-rubucen sun hada da kiraye-kiraye na tsagaita wuta mai dorewa, kawo karshen mamayar, da kuma dage shingen da akayi wa Gaza, da kuma amincewa da hakkokin ‘yan gudun hijirar Falasdinu.
Ofishin Jakadancin Falasdinawa a Rasha, tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Harkokin Waje ta Rasha, Kungiyar Kasashen Larabawa, da Majalisar Dinkin Duniya, sun kuma yi bikin Ranar Hadin Kai ta Duniya ga Al’ummar Falasdinawa.
29 ga Nuwamba, wadda aka fi sani da Ranar Hadin Kai ta Duniya ga Al’ummar Falasdinawa, ya zama abin tunatarwa ga duniya don tallafawa hakkokin Falasdinawa, gami da kudurinsu na samun ‘yancin kai, da hakkin komawa kasarsu.
A wannan karon, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya sake nanata cewa al’ummar Falasdinawa suna da cikakken ‘yancin ikon cin gashin kansu.