Ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya gana da takwaransa na Turkiya Hakan Fidan da safiyar Lahadi a nan birnin Tehran.
Ministan harkokin wajen na Turkiya ya kawo ziyarar Iran ne domin tattauna hanyoyin bunkasa alaka a tsakanin kasashen biyu da kuma tattauna halin da ake ciki a wannan yankin na yammacin Asiya.