An Yi Gagarumin Taron Ashura A Birnin Beirut Na Kasar Lebanon

Dubun dubatar mutanen kasar Lebanon sun yi gangamin taron raya ranar Ashura ta shahadar Imam Hussain ( a.s) a unguwar Dhahiya wacce aka sauya wa

Dubun dubatar mutanen kasar Lebanon sun yi gangamin taron raya ranar Ashura ta shahadar Imam Hussain ( a.s) a unguwar Dhahiya wacce aka sauya wa suna zuwa unguwar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah.

Mahalarta taron sun daga hotunan Sayyid Hasrallah wanda a shekarar da ta wuce yana raye, ya kuma gabatar da jawabi a wurin jimamin Ashura. Haka nan kuma sun rika bayar da taken da yake cewa: ” Muna Akan Riko Da Alkawali Ya Nasrallah.”

A yau 10 ga watan Muharram ne dai al’ummar musulmi Mabiya mazhabar Ahlul bayti suke tunawa da shahadar Imam Hussain ( a.s) da iyalansa da kuma sahabbansa madaukaka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments