An tsare tsohuwar shugabar kula da manufofin ketare ta EU Mogherini bisa badakalar cin hanci

Wata sabuwar badakala ta sake bata sunan kungiyar Tarayyar Turai, inda ‘yan sanda suka farmawa gidan toshuwar shugaban kula da manufofin harkokin wajen na kungiyar

Wata sabuwar badakala ta sake bata sunan kungiyar Tarayyar Turai, inda ‘yan sanda suka farmawa gidan toshuwar shugaban kula da manufofin harkokin wajen na kungiyar Federica Mogherini, tare da tsare ta a ranar Talata, a Belgium.

Mogherini wacce ta yi aiki a mukamin tun daga 2014 zuwa 2019, Ita da wasu abokan aikinta biyu ana binciken su kan yadda aka yi amfani da kudaden Tarayyar Turai ba bisa ka’ida ba, cin hanci da rashawa.

Federica Mogherini, jami’ar diflomasiyya ‘yar Italiya mai shekaru 52, ana tsare da ita tare da Stefano Sannino, babban jami’i a Hukumar da kuma mataimakin darakta na Kwalejin Turai.

An kama su, su ukun a wani bangare na binciken da Ofishin Mai Gabatar da Kara na Tarayyar Turai ya jagoranta.

Binciken ya shafi zargin nuna fifiko wajen bayar da shirin horo ga jami’an diflomasiyya.

Ofishin Mai Gabatar da Kara na Tarayyar Turai ya zarge su da “zamba wajen bayar da kwangilolin gwamnati, cin hanci da rashawa, inda ‘Yan sandan Belgium suka gudanar da jerin bincike a ranar Talata a hedikwatar Hukumar Kula da Harkokin Waje ta Tarayyar Turai, a gine-gine da dama na Kwalejin Turai da ke Bruges, da kuma gidajen wadanda ake zargin su uku uku.

Dama dai a cfen baya an gano tarin takardun kudi na Yuro a gidajen ‘yan majalisar dokoki na turai, tare da kyaututtuka daga Qatar, Mauritania, da Morocco. Lamarin da ya girgiza Majalisar Dokokin Turai matuka a watan Disamba na 2022. Ana zargin ‘yan majalisar wakilai da mataimakan majalisar dokoki da dama da karbar cin hanci da rashawa a madadin tasirinsu kan wasu shawarwari na majalisar.

Akwai wasu badakaloli da dama da ake yawan samu a cikin kasashen Turai, musamman game da karkatar da kudaden EU.

A cewar sabon rahoto daga Ofishin Mai Gabatar da Kara na Tarayyar Turai, amfani da kudaden EU ba bisa ka’ida ba ya zama ruwan dare a kasashe 27 na Tarayyar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments