An Tattauna Ta Wayar Tarho Tsakanin Putin Da Muhsin Riza’i

an yi tattaunawa ta wayar tarho tsakanin shugaban raasha da sakataren majlisar tsaron kasar iran kan muhimman batutuwa

Babban sakatare majalisar koli ta tsaron kasa muhisn Rizai ya tattauna ta wayar tarho da shugaban kasar rasha vladmir putin kan bukatar da ake da ita ta yadda kasashen biyu za su ci gaba da yin aiki tare bisa taswirar da suka tsara yadda za su ci gajiyar juna

A tattaunawar tasu ta wayar tarho a jiya litinin babban sakataren majalisar tsaron kasa tsakaninsa da shugaban rasha putin sun kuma tattauna kan muhimman batutuwan da suka faru a baya bayan nan a yankin da ma kasa da kasa, sai dai sun fi mayar da hankali kan yanayin da ake ciki a yanmacin asiya.

Rezaei ya nuna farincikinsa game da matsayar shugaban na rasha da ma sauran jami’an kasar game da yadda suka jinjina irin rawar da jagoran juyin musulunci na iran shahid Ayatullah sayyid Ali khamna’I ya taka da ma sauran gwarazan kasar da suka yi shahada

A watan maris shugaban kasar rasha  yace kashe jagora ayatollah sayyid Ali khamna’I  ya zama take hakki ne a fili na dukkan kaidojin dabiun dan adam da kuma dokokin kasa da kasa

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted