An Sanar Da Nadin Sabon Shugaban Hedkwatar Khatamul Ambiya A Iran.

Rahotanni sun bayyana cewa sanar da sabon kwamandan hedkwatar khatamul ambiya na nuna irin sabbin canje –canje da irin tsari da ta bullo da shi

Rahotanni sun bayyana cewa sanar da sabon kwamandan hedkwatar khatamul ambiya na nuna irin sabbin canje –canje da irin tsari da ta bullo da shi kan abubuwan da ta fi bawa muhimancin, kuma wata babbar cibiya da ake sa ido kan tsaron kasa, canjin jagoranci na iya yin tasiri babba a bangaren soji wajen tunkarar kalubalen da take fuskanta a bangarori daban daban.

Major ganaral Ali Abdullahi sabon kwamandan hekdawatar khatamul Ambiya ya jaddada a bayanin da ya fitar cewa sojojin kasar Iran a shirye suke su kare kasar daga duk wata barazana, da kuma kare dukkan ababen girmamawa na kasar,

Ya kara da cewa a halin yanzu sojojin  kasar sun fi zama cikin shirin ko ta kwana fiye da lokacin yakin kwanaki 12 domin sun mallaki muhimman kayan aiki  da za su yin nasara kan duk wanda suka tunkara,

Daga karshe Abdullahi ya isar da sakon taya murnan game da zagayowar ranar haihuwar manzon rahama da kuma makon hadin kai ga dukkan alummar kasar iran adai dai lokacin da ake gudanar da tarurrukan makon yadin kai a kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted