An samu gobara a wasu matatun mai guda biyu na Iran bayan harin da Isra’ila ta kai

Wasu Hare-haren da gwamnatin Isra’ila ta kai ya haddasa gobara a wasu matatun mai a lardin Bushehr da ke kudancin kasar Iran. Gobarar ta tashi

Wasu Hare-haren da gwamnatin Isra’ila ta kai ya haddasa gobara a wasu matatun mai a lardin Bushehr da ke kudancin kasar Iran.

Gobarar ta tashi ne a wurin a ranar Asabar bayan da wasu kananan jiragen yakin Isra’ila guda biyu suka kai hare-hare a kan kayayyakin sarrafa iskar gas da ke yankin kudancin Pars.

Hare-haren sun yi haddassa fashe fashe a matatar iskar gas ta Fajr-e Jam, daya daga cikin mafi girma a Iran, da kuma wata karamar matatar mai a mataki na 14 na tashar iskar gas ta Kudu Pars.

Har yanzu ba a fitar da kiyasin barnar a hukumance ba.

Bayan gobarar, ma’aikatar mai ta Iran ta fitar da wata sanarwa inda ta tabbatar da harin.

Sanarwar ta ce, nan da nan aka kaddamar da aikin shawo kan gobarar da dakile ta.”

Matatar man ta Pars ta kudu ita ce tashar iskar gas mafi girma a duniya, wacce ke kan iyakar teku tsakanin Iran da Qatar.

Ta kunshi sama da kashi 70% na bukatun iskar gas na Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments