An sake zabar Eto’o a matsayin Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Kamaru  

A Jamhuriyar Kamaru, an sake zabar Samuel Eto’o a matsayin Shugaban Hukumar kwallon kafa ta kasar (Fecafoot) Duk da kin amincewa da Ma’aikatar Wasannin kasar

A Jamhuriyar Kamaru, an sake zabar Samuel Eto’o a matsayin Shugaban Hukumar kwallon kafa ta kasar (Fecafoot) Duk da kin amincewa da Ma’aikatar Wasannin kasar ta yi.

An sake zabar Eto’o ne wanda shi ne Tsohon kyaftin din kungiyar Indomitable Lions ne a wani wa’adi na tsawon shekaru hudu a kasa da shekaru hudu bayan ya hau kan karagar shugabancin Hukumar.

Saidai ma’aikatar Wasanni ta kasar ta nuna matukar adawa da zaben wanda ta a matsayin wanda bai dace ba.

A nata bangaren, hukumar ta Fecafoot, ta sake nanata cewa dokokin FIFA sun haramta duk wani tsoma baki na siyasa a cikin harkokin wassani.

Zaben ya gudana ne a gaban wakilan FIFA da CAF, wadanda suka kasance a wurin don sa ido kan tsarin da kuma tabbatar da bin ka’idoji.

Tun daga wa’adinsa na farko, Samuel Eto’o ya fuskanci suka mai yawa game da yadda yake tafiyar da harkokin kwallon kafa na Kamaru, musamman gazawar tawagar kasar na cancantar shiga gasar cin kofin duniya na 2026 da kuma takaddama da Ma’aikatar game da zabar kocin ‘yan wasan kasar na Indomitable Lions.

Samuel Eto’o dai ya lashe kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa na Afirka na shekara har sau hudu yana kuma har yanzu yana da isasshen goyon baya don ci gaba da jagorantar hukumar ta FECAFOOT.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments