Kafafen watsa labarun Amurka sun sanar da cewa wani karamin jirgin sama ya fadi akan wata cibiyar kasuwancin dake Philadelphia a jihar Pennsylvania tare da kashe mutane 6 da suke cikinsa.
Kafafen watsa labarun na Amurka sun ce ‘yan kwana-kwana sun yi kokarin kashe gobarar da ta tashi a cikin gidaje da dama a yankin da jirgin ya fado.
Tashar talabijin din “Fox News” ta sanar da cewa jirgin da ya fado na jigilar marasa lafiya ne, yana dauke da wani mara lafiya daya da dan’uwansa, sai kuma likitoci biyu da suke tare da shi.
Ita kuwa jaridar “Philadelphia Enquiry” ta ambato ‘yan sanda suna cewa, jirgin ya fado ne da misalin karfe 6;pm agogon yammacin gabashin Amurka.
A ranar Larabar da ta gabata ma an sami hatsarin jirgin sama na matafiya wanda ya ci karo da wani jirgin soja mai saukar angulu da hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 67, wanda ake dauka a matsayin daya daga cikin mafi munin hatsarin jiragen sama da aka yi a Amurka a cikin shekaru 25.