Sabon shugaban kasar Mozambique Daniel Francisco Chapo, ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasar na 5, a wani biki da aka gudanar jiya Laraba a filin taro na “Independence Square”, wanda ke birnin Maputo, fadar mulkin kasar.
Cikin manyan baki da suka halarci bikin rantsuwar har da tsofaffin shugabannin kasar Joaquim Chissano, da Armando Guebuza, da shugaban kasar mai barin gado Filipe Nyusi, Akwai kuma shugaban Afirka ta kudu.
Cyril Ramaphosa, da na Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embalo, da sauran baki sama da 2,000, da suka hada da wakilan gwamnatoci, da na hukumomi, da abokan hadin gwiwar kasar, da sauransu.
Cikin jawabinsa na kama aiki, mista Chapo ya sanar da shirin gwamnatinsa na gudanar da sauye-sauye, ciki har da rage adadin ma’aikatu, da soke mukamin mataimakin minista, da karkata albarkatu zuwa muhimman sassan gwamnati.