A karon farko hukumomin Ireland sun amince da nada jakadan Falasdinu a wannan kasa.
A rahoton Al Jazeera, Ireland ta amince a karon farko da nada jakadan Falasdinu a wannan kasa.
Majiyoyin gwamnati sun sanar da cewa Jilan Wahba Abdul Majeed, wanda a halin yanzu yake jagorantar tawagar Falasdinawa a Ireland, zai karbi sabon mukamin.
Norway, Spain da Jamhuriyar Ireland sun sanar a watan Yunin wannan shekara cewa sun amince da Falasdinu a matsayin kasa mai cin gashin kanta.
Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta fitar da wata sanarwa da kakkausar murya ta yi Allah wadai da wannan hukunci tare da bayyana hakan a matsayin tukwici na “ta’addanci” a tsakiyar yaki.
Gwamnatin Falasdinu ta kuma bayyana a watan Oktoban da ya gabata cewa, tana shirin kara fadada huldar diflomasiyya da kasar Ireland daga tawagar diflomasiyya zuwa ofishin jakadanci, kuma a yanzu ta zabi jakadan kanta a wannan kasa.
Kasashe 144 daga cikin kasashe 193 na Majalisar Dinkin Duniya, wadanda suka hada da galibin kasashen kudancin duniya, Rasha, China, Indiya da Iran, sun amince da Falasdinu a matsayin kasa.