An kori jakadan Isra’ila a Habasha daga taron Tarayyar Afirka

An kori jakadan Isra’ila a Habasha Avraham Neguise daga taron kungiyar Tarayyar Afirka da aka gudanar a wannan Talata a Addis Ababa domin tunawa da

An kori jakadan Isra’ila a Habasha Avraham Neguise daga taron kungiyar Tarayyar Afirka da aka gudanar a wannan Talata a Addis Ababa domin tunawa da kisan kiyashin da aka yi a Rwanda.

An fitar da Neguise daga dakin taro na Mandela da ke hedikwatar Tarayyar Afirka bayan da kasashe da dama suka nuna rashin amincewarsu da halartarsa a taron shekara-shekara kan kisan kiyashin da aka yi a kasar Rwanda.

Jakadan na Isra’ila ya shiga wurin taron ne ba zato ba tsammani, ba tare da an gayyace shi ba, a cewar majiyoyin diflomasiyyar da suka halarci taron.

Majiyar ta kara da cewa tawagogin kasashen Afirka da dama sun nuna rashin amincewa da zuwansa, lamarin da ya sa aka dakatar da taron har sai da ya fita.

Rahotanni sun ce kungiyar Tarayyar Afirka na gudanar da bincike domin gano wanda ya gayyace shi.

Kungiyar fafutukar neman ‘Yancin Falasdinu (PLO) ita ce kungiya ta farko da aka baiwa matsayin mamba mai sa ido a cikin  Tarayyar Afirka a shekarar 1973, kuma tana ci gaba da samun goyon baya mai karfi daga yawancin kasashen Afirka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments