An Kira Yi Gwamnatin Canada Da Ta Kama Olmert Da Livini Na “Isra’ila

Kungiyoyin kare hakkin bil’adama na kasar Canada sun shigar da kara ga jami’an ‘yan sandan kasar, da kuma ma’aikatar shari’a da su kama tsohon Fira

Kungiyoyin kare hakkin bil’adama na kasar Canada sun shigar da kara ga jami’an ‘yan sandan kasar, da kuma ma’aikatar shari’a da su kama tsohon Fira ministan haramtacciyar kasar Isra’ila Ehud Olmert da kuma ministar harkokin waje Tzipi Livni bisa rawar da su ka taka baya a laifukan yaki a Gaza a tsakanin 2008-2009.

Kungiyoyin sun bukacin ganin an fitar da sammacin kamo ‘yan sahayoniyar biyu a bisa dogaro da dokokin kare hakkin dan’adama da laifukan yaki na kasar Canada, saboda kasar tana karkashin yarjejeniyar Geneva ta 4 da ta bukaci kasashe su hukunta masu irin wadannan laifukan.

Bugu da kari, kungiyoyin sun ce Olmert wanda ya yi fira minista daga 2006 zuwa 2009, shi ne mai rike da mukami na koli a  lokacin hare-haren soja da su ka kashe fararen hula da lalata muhimman cibiyoyi. Haka nan kuma a wancan tsakanin sojojin Haramtacciyar kasar Isra’ila sun yi amfani da makamin Phosphorus mai fitar da farin hayaki da aka haramta amfani da shi a yake-yake. Sojojin na mamaya sun kuma rusa gidaje da lalata tsarin magudanan ruwa na kiwon lafiya, kamar kuma yadda su ka yi wa fararen hula da dama kisa ba tare da shari’a ba. Bugu da kari, sun hana shigar da kayan agaji zuwa yankin Gaza a wancan lokacin.

Ita kuwa Livini ta kasance memba a cikin karamar majalisar tsaro wacce ta taka rawa wajen shatawa sojoji ta’asar da su ka yi, ta kuma furta cewa, martanin da ya kamata “Isra’ila” ta mayar wa Falasdinawa ya kamata ya zama ” Na Hauka.”

Dama dai mutanen biyu suna da wata shari’ar da aka kai su kara a gaban kotuna daban-daban na kasashen turai. Kuma a 2009 ne wata kotu a Birtaniya ta fitar da sammaci a kamo su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted