An Kashe ‘Yan Kungiyar Shabab 19  A Kasar Somaliya

Sojojin kasar Somaliya sun sanar da kai wani farmaki a kudancin kasar da ya yi sanadiyyar kashe 19 daga cikin ‘yan kungiyar ‘al-shabab’.  Sanarwar wacce

Sojojin kasar Somaliya sun sanar da kai wani farmaki a kudancin kasar da ya yi sanadiyyar kashe 19 daga cikin ‘yan kungiyar ‘al-shabab’.

 Sanarwar wacce tashar talbijin din ‘almayadin’ ta nakalto ta ce, sojojin na Somaliya sun kai harin ne a jiya Litinin da dare a yankin Jubayi, wanda kuma bayan kashe ‘yan kungiyar an kuma jikkata wasu da dama.

Ma’aikatar tsaron kasar Somaliya ta kuma ce; sojojin kasar sun yi nasarar kama makamai masu yawa a tare da kungiyar ta ‘al-shabab’.

 A cikin watan Disamba na shekarar da ta shude ma dai sojojin na Somaliya su ka yi nasarar kashe ‘yan kungiyar su 130 a jahohin Gulmadag, da Jubaland.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments