An Kashe Sojojin HKI 3 A Yankin Khan-Yunus Na Gaza

Da safiyar Yau Lahadi Adadin sojojin mamaya na HKI da aka kashe a yankin Khan-Yunus sun kai 3. Jaridar Yediot Ahranot ta ‘yan sahayoniya ta

Da safiyar Yau Lahadi Adadin sojojin mamaya na HKI da aka kashe a yankin Khan-Yunus sun kai 3.

Jaridar Yediot Ahranot ta ‘yan sahayoniya ta buga labarin cewa; An kuma kashe waji jami’in soja na rundunar Gulani ta hanyar fashewar nakiya da aka dasa akan hanyar motarsa a jiya Asabar a Kudancin Gaza.

Har ila yau jaridar ta ce, an kuma jikkata wani jami’in sojan mamayar bayan da nakiya ta daki wata motar jigilar sojoji.

A nata gefen, rundunar Kassam ta kungiyar Hamas ta sanar da kai wa motar daukar sojojin HKI hari ta hanyar nakiyar da ta dasa a gidan gaban motar.

Bugu da kari dakarun na Kassam sun sanar da kai wani harin akan motar soja ta 3 ta hanyar amfani da makamin “al-Yassin 105” a yankin Abasan al-Kabirah dake Khan Yunus.

Haka nan kuma dakarun na Kassam sun ce, mayakansu sun ga yadda sojojin na mamaya su ka binne motocin da su ka kone, da kuma saukar jiragen sama masu saukar angulu domin daukar gawawwaki da wadanda jikkata.

Duk da cewa sojojin na HKI sun dauki shekaru biyu suna kisan kiyashi a Gaza, sai dai duk da haka bai hana ‘yan gwgawarmaya fitowa suna kashe su da jikkata su ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted