Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa, an kashe sojoji 2 a yankin kusa da Tubas dake Arewacin yammacin kogin Jordan.
Kafafen watsa labarun sun kuma ce, maharin ya isa wani shinge na soja dake kusa da Tayasir, ya kuma boye a cikin hasumiyar da masu tsaro ke zama a ciki, sannan ya bude wa sojoji wuta daga sama.
Har ila yau maharin ya yi bata-kashi da sojojin da suke a wajen, sai dai a karshe sun ci karfinsa, da hakan ya yi shahadarsa.
A bayanin da kungiyar Hamas ta fitar ta jininawa maharin tare da cewa, abinda hakan yake nufi shi ne cewa hare-haren da ‘yan sahayoniya suke kai wa ba za su tafi haka kawai ba tare da mayar da martani ba.
Ita ma kungiyar “ Jabahatu-tahrir Falasdin” ta sanar da cewa; Harin yana kara tabbatar da cewa, tsaron ‘yan mamaya yana da rauni, kuma ba za ta iya jurewa a gaban gwgawarmaya ba.
Wannan harin dai yana zuwa ne a lokacin da ‘yan sahayoniya suke cigaba da yi wa al’ummar Falasdinu kisan kiyashi da kuma barnata gidajensu.
A ranar Litinin din da ta gabata, sojojin mamayar sun kashe Falasdinawan da sun kai 70 a sansanin ‘yan hijira na Jenin. Dama tun a ranar Asabar sojojin HKI sun rusa gidajen Falasdinawa da sun kai 100 a sansanin na Jenin.