An kashe sojan HKI guda a safiyar ranar Lahadi bayan da wani ba falasdine mai tuka babbar mota ya Burma motarsa kan gungun sojojin HKI a wani yanki kusa da Qalqelia na yankin yamma da kogin jorda. Ya kara da cewa kafin haka sojojin HKI sun kashe Falasdinawa da dama a yankin yamma da kogin Jordan kuma sun ci gaba da kisa da kuma rusa gidajen mutane a yankin tun bayan fara yakin tufanul Aksa.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nalaklto majiyar yahudawan na cewa sojan da aka kashen shi ne Staff Sergeant Inbar Avraham Kav , dan shekara 20 a duniya daga rundunar battalion ta 890.
Yan kwana-kwana sun dauke shi zuwa asbita amma likitoci sun kasa ceton ransa. Sannanan ba falasdinen da ya yi wannan aikin dan garin Hit ne da ke kusa da Qalqelia a yankin yamma da kogin Jordan.
Tun bayan yakin tufanul aksa, sojojin HKI suke kashe falasdinawa da rusa gidajensu da kuma korarsu daga yankin . an kiyasta cewa tun lokacin zuwa yanzu yahudawan sun kori falasdinawa daga yankunan yamma da kogin Jordan har kimani 4000. Kungiyar Hamas ta yaba da aikin daukar fansan a kusa da garin qalqilia.