An Kashe Mutum Guda A Harin Isra’ila (HKI) A yankin Duddan Golan Na Siriya

Akalla mutum daya ne ya rasa ransa a yankin Qunaitra na kasar Siriya a lokacinda HKI suka kai hare-hare a yankin da jirgin yaki wanda

Akalla mutum daya ne ya rasa ransa a yankin Qunaitra na kasar Siriya a lokacinda HKI suka kai hare-hare a yankin da jirgin yaki wanda ake sarrafashi daga nesa wato Drons.

Kamfanin dillancin labaran SANA na gwamnatin kasar Siriya ya bayyana cewa majiyar yankin wanda yake kudu maso yammacin duddan Golan wadanda HKI ta mamaye, ya bayyana cewa tun bayan kifar da shugaba Asad a shekarar da ta gabata, sojojin HKI sun kai hare-hare kan dukkan rumbun ajiyar makamai na sojojin Bashhar Al-asad, kuma su kan kai hare-hare da dare a kan yankun dukkan Golan na kasar siriya wanda yaejeniyar 1974 ya bayyana a matsayin yankin babu makamai. Sannan sukan kai hare hare kan yankin Suwaida su kashe wanda suka ga dama.

Yan ta’adda na kungiyar tahrirusham masu iko da kasar sun fafata da mabiya mazhabar Duruss a yankin Suwaida na kasar da sunan wai sun yi tawaye, alhali yan ta’addan masu kafirta musulmi basu yarda cewa su musulmi ne ba.

Sana ya kara da cewa mutanen yankin wadanda basa son a bayyana sunayensu sun bayyana masa cewa, sojojin yahudawa sun kai hari a kan wani gida a kauyen Turnejeh da ke arewacin Qunaitra a dareh jiya Talata sun kashe wani matashi a gidan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted