An Kashe Mutane Da Dama A Tsakiyar Najeriya

Wasu masu dauke da makamai sun kai hari a wasu kauyuka biyu dake jihar Filato inda su ka kashe mutane 52. Rahotannin da suke fitowa

Wasu masu dauke da makamai sun kai hari a wasu kauyuka biyu dake jihar Filato inda su ka kashe mutane 52.

Rahotannin da suke fitowa daga jihar ta Filato sun ambaci cewa wasu makiyaya ne su ka kai  harin na ranar Litinin din da ta gabata an kai shi ne a kan yankin Bassa.

Kamfanin dillancin labarun Reuters da ya dauki labarin ya ambaci cewa,an gano gawawwaki 51 daga cikin wadanda aka kashe din, kuma wani adadi mai yawa na mutanen kauyukan sun jikkata.

Ita kuwa kungiyar “Amnesty International” ta ambaci cewa maharan sun kuma rusa gidaje, tare da wawashe kayan da suke cikinsu. Kungiyar ta zargi jami’an tsaron kasar da gajiyawa wajen tabbatar da tsaro.

Jahar Filato ta dade tana fuskantar fadace-fadace a tsakanin makiyaya da mazauna  kauyuka, duk da cewa daga baya an sami lafawar al’amurran,amma daga baya ya sake dawowa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments