An Kashe Adadin Fararen Hular Da Bai Gaza 55 Ba A Arewacin Congo

Kungiyoyin da suke dauke da makamai sun kashe fararen hular da ba su gaza 55 ba a wani hari da su ka kai wa wasu

Kungiyoyin da suke dauke da makamai sun kashe fararen hular da ba su gaza 55 ba a wani hari da su ka kai wa wasu kauyuka da sansanin ‘yan hijira a Arewacin DRC.

Mahukunta a yankin na Arewacin DRC sun ambaci cewa wasu masu dauke da makamai na kungiyar CODECO sun kai wa wasu kauyuka da suke yankin Djaiba hare-hare a gundumar Ituri a  jiya litinin da dare.

Bugu da kari masu dauke da makaman sun kai hari a cikin sansanin ‘yan hijira da suke a cikin wannan yankin kamar yadda shugaban sansanin Antoinnette Nzale ya fadawa manema labaru.

Ita dai kungiyar CODECO  gamayya ce ta kungiyoyin da suke dauke da makamai da su ka fito daga kabiluar Landu, manoma. Shekaru 4 da su ka gabata wannan kungiyar ta kai wasu hare-hare da ta kashe mutane 1,800 tare da jikkata wasu 500 a shekarar 2022.

MDD ta ce wannan harin za a iya daukarsa a matsayin  laifi akan bil’adama.

Nzake ya ce; sun kai wa dukkanin kauyukan da suke a yankin hari,” sannan ya kara da cewa; Dakarun tabbatar da zaman lafiya na MDD da ake kira; Monusco, tare da sojojin gwamnatin Congo, sun yi kokarin hana hare-hare amma masu dauke da makaman sun fi karfinsu. A watan Satumba da shekarar da ta kare ma, wannan kungiyar ta CODECO ta kai harin da ta kashe mutane 20 a garin Djugu, wanda shi ne garin da ta kai wa hari a wannan Litinin din da ta gabata.

A can gabashin kasar ta Congo ma dai  kungiyar M 23 mai samun goyon bayan Rwanda ta kwace iko da garin Goma mai muhimmanci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments