Fafa roma Farancis shugaban cocin catholica ya koma makwancin na din din din a Santa Maria Maggiore Basilica, wanda kuma ake kira St. Mary Major, daya daga cikin fitattun coci-coci guda 4 mafi daraja a birnin Vatican .
Shafin yanar gizo na labarai ‘Afrika News’ ya bayyana cewa Farancis shi ne paparoma na farko daga yankin Laten Amurka, wanda kuma ya kirkiro abubuwa da dama a cocin daga ciki shi ne ya fara zaben inda za’a yi masa kabari. Kuma shi ne ya fara zaben a bisneshi a wajen birnin Vatikan tun shekaru fiye da 120 da suka gabata. Wato tun bayan Paparoma Leo 13.
Tashar talabijin ta CNN ta nakalto cewa fafaroman ya bukaci a yi masa kabari mai sauki a wajen birnin Roma wato Basilica di Santa Maria Maggiore.