Jami’an tsaron kasar Tanzania sun yi awon gaba da fitaccen dan siyasar kasar Freeman Mbowe tare da wasu shugabannin jam’iyyarsa ta Chadema.
An kama Freeman ne dai a yankin Kudu maso yammacin kasar a jiya juma’a, kamar yadda kafafen watsa labaru su ka ambata.
Majiyar ta ce ana zargin Freeman ne da karya dokokin yakin neman zabe a yankin da aka kama shi, sai dai ‘yan hamayyar sun yi watsi da zargin na jami’an tsaro, suna masu cewa manufar kama su shi ne dakile armashin yakin neman zaben da yake yi.
Wannan dai ba shi ne karon farko da aka kama shugaban jami’iyyar adawar ta Chadema ba. A watan Satumba ma an kama shi tare da mataimakinsa Tundu Lissu da kuma wasu ‘yan hamayyar siyasar.
A farkon shekarar 2025 mai zuwa ne za a yi zaben shugaban kasar ta Tanzania da Freeman yake takara.