Mahukunta a kasar Syria sun kafa dokar hana zirga-zirga a yankin Dar’a dake kudancin kasar Syria.
Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta ambato cewa; jami’an tsaron kasar ta Syria sun kafa dokar ta baci a yankin “Basra-sham’ dake yankin Dar’a.
Sai dai har yanzu babu wani cikakken bayani akan dalilin da ya sa aka kafa wannan doka, amma wasu majiyoyin sun ambaci cewa a cikin kwanakin bayan nan an sami rikice-rikice a yankin.
Wasu majiyoyin sun ambaci cewa wasu masu dauke da makamai sun yi harbe-harbe a yankin wanda ya yi sanadiyyar jikkata mutane biyu a garin Basras-sham.