A Faransa an sake jibge jami’an tsaro 70,000 gabanin sabuwar zanga zangar tsadar rayuwa da aka shirya gudanarwa yau Asabar.
Ministan Harkokin Cikin Gida na Faransa Laurent Nuñez ya sanar a ranar Juma’a cewa za a tura jami’an ‘yan sanda da na Jandarma 70,000 a fadin kasar a ranar Asabar, don tunkarar zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa.
Da yake bayyana hakan a wata hira da tashar BFMTV, ministan ya tabbatar da cewa adadin jami’an da za a tura zai yi daidai da ranar Asabar da ta gabata.
Yau sama da wata guda Kenan da jerin kungiyoyin kwadago a faransa ke zanga zanga kan tsadar rayuwa da hauhawan faranshin makamashi.
Kungiyoyin na neman a dauki mataki na rage farashin makamashi da abinci, sannan suna neman karin albashi da fansho, samun gidaje.
Kungiyoyin kwadago da na matasa da dalibai na daga cikin wadanda suka kira zanga zangar.
Bayanai daga Faransar na cewa mutane 7,184 aka kama tun bayan soma zanga zangar tsadar rayuwa a fadin kasar a a ranar 17 ga Oktoba.
Jerin kungiyoyi a faransa sun shiga zanga zangar tsadar rayuwa da hauhawan farashin makamashi wacce ta samo asali daga fishin daliban makarantun sakandare dake zargin gwamnati da gazawa wajen warware matsalolin da suka dabaibaiye sha’anin ilimi a kasar.
Zanga zangar ta hada daliban makarantar sakandare, daliban jami’a, wadanda sukayi ritaya, da ma’aikatan kamfanoni masu zaman kansu, bisa ga kiran kungiyoyin kwadago na gwamnati.