An Halaka Sojojin HKI Biyu Ta Hanyar Sukarsu Da Wuka A Kusa Da Iyakar Jordan

A yau Alhamis ne ne aka kai wasu hare-hare biyu na suka da wuka akan mashigar ‘al-karamah’ dake kan iyakar Falasdinu da Jordan. Majiyar ‘yan

A yau Alhamis ne ne aka kai wasu hare-hare biyu na suka da wuka akan mashigar ‘al-karamah’ dake kan iyakar Falasdinu da Jordan.

Majiyar ‘yan sahayoniya wacce ta ambaci labarin ta kuma ce; A matakin farko an kai hari ne ta hanyar bude wuta da bindiga akan sojoji, sannan aka kai wani harin ta hanyar sara da wuka.

Harin ya yi sanadiyyar kashe sojoji biyu da kuma jikkata wasu da dama.

Jim kadan bayan kai wannan harin ne dai,sojojin HKI su ka killace yankin baki daya domin yin bincike.

A cikin watan Satumba an kai wani harin irin wannan wanda ya yi sanadiyyar halakar ‘yan sahayoniya 3 da kuma jikkata wasu da dama.

Wannan harin na ‘yan gwagwarmaya ya zo ne  a lokacin da HKI take ci gaba da yi wa al’ummar Falasdinu a Gaza kisan kiyashi wanda ya karaci shekara ta uku.

A cikin makon da ya shude kawai, an kai hare-hare na gwagwarmaya da sun kai 63 kan sojoji da cibiyoyin mamaya a tsakanin Gaza da yammacin Kogin Jordan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted