An Gudanar Gagarumar Zanga Zangar Goyon Bayan Falasdinawa A Australia Da Indonasia

Duban dubatan mutane sun gudanar zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa da kuma yin tir da kokarin samar da huldar jakadanci da HKI a maida kome kamar

Duban dubatan mutane sun gudanar zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa da kuma yin tir da kokarin samar da huldar jakadanci da HKI a maida kome kamar ba abinda ya faru. Sun kuma bayyana tsagaita wutan da aka samar da Hamas tana tangal tangal saboda tun farko ba’a gina shi kan yadda zata dore ba.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto masu zanga-zanga suna cewa, wannan sulhun da kasashen yamma suka kulla da Hamas wani makirci ne na kara samun iko kasashen musulmi da ma wasu kasashen wadanda ban a musulmi ba.

Sun kuma bayyana cewa, bayan shekaru biyu da kissan kiyashi sun samar da abinda suka kira sulhu ne na wani lokaci, amma zaman lafiya ba zata taba dorewa ba sai an kafa kasar Falasdinu mai zaman kanta kuma mai cikekken iko.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments