An gudanar da janazar babban kwamanda a kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Ibrahim Akil a yankin kudancin birnin Beirut fadar mulkin kasar Lebanon a wanann Lahadi.
A yayin taron janazar wadda manyan kusoshin kungiyar suka halarta da suka hada da mataimakin bababn sakataren kungiyar Sheikh Naim Qassem, an gabatar da jawabai dangane da sabon matakin da aka shiga na yaki tasakanin kungiyar da kuma Haramtacciyar Kasar Isra’ila.
Mataimakin bababn sakatare kungiyar ya gabatar da jawabi mai zafi kan ayyukan ta’addancin da gwamnatin yahudawan take aikatawa a cikin kwanakin nan a kasar Lebanon, inda yace tabbas an shiga wani sabon babi na gwagwarmaya tsakaninsu da Isra’ila.
Ya kara da cewa, sun zaton cewa ta hanyar daukjar irin wadanann matakai an yin kisan killa a kan jagorori da kwamandoji na kungiyar Hizbullah zasu iya dakile ayukan kungiyar ko sanya tat a yi rauni, ya ce to tabbas suna yin kore a kan wannan tunani nasu.
Ibrahim Akil tare da wasu kusoshi na Hizbullah sun yi shahada a ranar Juma’a da gabata, biyo bayan harin da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kaddamar kan yankin kudancin birnin Beirut.