Gagarumar zanga-zangar goyon bayan Falastinu a kasar Jordan

Dubban mutane ne a birnin Amman babban birnin kasar Jordan suka gudanar da zanga-zanga bayan sallar Juma’a domin yin Allah wadai da sake dawo da

Dubban mutane ne a birnin Amman babban birnin kasar Jordan suka gudanar da zanga-zanga bayan sallar Juma’a domin yin Allah wadai da sake dawo da laifukan da Isra’ila ke aikatawa a Gaza.

A rahoton factjo, dubban mutane sun bayyana goyon bayansu ga al’ummar Gaza a wani gagarumin maci na wannan Juma’a.

Mahalarta tattakin sun yi Allah wadai da hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai kan masallacin Al-Aqsa a cikin watan Ramadan.

 A cikin wannan maci da aka gudanar bisa gayyatar Harkar Musulunci da kwamitin Tallafawa Falastinawa suka kira, dubban mutane sun halarta da suka hada da wakilai na siyasa, jam’iyyu, da kungiyoyin kwadago, da sauran jama’ar kasa, inda suka yi ta rera taken la’antar ayyukan zalunci na gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila, da kuma kin amincewa da duk wata makarkashiyar da aka kulla domin korar Falastinawa daga yankunansu.

Haka nan Wadanda suka halarci tattakin sun yi Allah wadai da kisan kiyashin da ake ci gaba da yi a zirin Gaza, tare da yin kira ga gwamnatocin kasashen Larabawa da na Musulunci da su dauki matakin gaggawa na dakatar da wannan aika-aikar da Isra’ila ke yi.

Mahalarta tattakin na nuna alhinin shahadar Abu Hamza, kakakin rundunonin Quds Brigade, sun yaba da karfin azamarsa da jajircewarsa, da sadaukar da ransa da jininsa saboda ‘yancin al’ummarsa.

Masu zanga-zangar sun kuma yi Allah wadai da cin amanar Amurkawa, wadanda suka bai wa makiya yahudawan damar soke yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kuma ci gaba da kashe al’ummar Gaza, tare da bayyana  gwamnatin Amurka a matsayin wadda take daukar nauyin wannan laifi ta hanyar aika bama-bamai da makamai masu linzami ga Isra’ila domin  kisan Falastinawa a zirin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments