Shugaban kasar Rasha Vladimit Putin ta tokwaransa na kasar China Xi Jinping sun tattauna a birnin Mosco a yau Alhamis, inda kasashen biyu suka kara dankon zuminci a tsakaninsu, da fatan zasu bukasa harkokin kasuwanci da ci gaba a tsakaninsu nan da shekara ta 2030.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa shugaba Xi Jinping ya je birnin Mosco ne don halattan bikin nasara da kasar Rasha ta samu kan sojojin Nazi a yankin duniya na biyu shekaru 80 da suka gabata.
Haduwar shugabannin kasashen biyu yana zuwa ne a dai-dai lojkacinda ake kara tada jijiyoyin wuta tsakanin su da kasashen yamma musamman Amurka.
Shuwagabannin biyu sun kara jaddada manufar su da samar da duniya mai kudubobi daban daban ba kasar Amurka kadai zata jujjuya duniyar kamar yadda ta ga dama ba.