Ministan Fetur na Iran Muhsin Fak Najad,ya fadawa manema labaru cewa an bude taron kungiyar ta kasashe masu arzikin iskar Gas, wacce aka fi sani da GECF. Ministan ya kara da cewa, a yayin wannan taron za a tattauna batutuwa da dama da su ka hada da kasuwanci da sauran batutuwa masu alaka da shi.
Za a dauki kwakani biyu ana yin taron kasashen masu arzikin iskar Gas a nan Tehran da suke ke da mafi yawancin Iskar Gasa a duniya,kamar yadda ministan na Iran ya ambata.
Bayan ga kasashen da suke mambobi a kungiyar da akwai wasu kasashen takwas masu sanya ido, sai kuma Kasar Oman a matsayin babbar bakuwa.
A yayin wannan taron za a zabi sabon babban magatakardar kungiyar da kuma hanyoyin tantance zama mamba a cikin wannan kungiya.