An Fara Musayar Fursinoni Tsakanun Hamas Da HKI A Safiyar Yau Litini

Labaran da suke fitowa daga kasar Falasdinu da aka mamaye sun nuna cewa kungiyar agaji ta Red Cross ta fara karban fursinoni yahudawa daga hannun

Labaran da suke fitowa daga kasar Falasdinu da aka mamaye sun nuna cewa kungiyar agaji ta Red Cross ta fara karban fursinoni yahudawa daga hannun kungiyar Hamas kamar yadda aka tsara.

Tashar talabijan ta Almayadeen ta bayyana cewa kungun fursinoni yahudawa masu rai 7 ne kungiyar ta Karba daga dakarun Hamas a yankin da ake kira Nitsarin a tsakiyar zirin gaza, da misalign karfe 8 na safe a yayinda gungu na biyu kuma wanda ya kunshi yahudawa 10 masu rai kungiyar Agajin ta karbesu a garin Khan Yunus dake areacin gaza da misalign karfe 10 na safe.

Labarin ya kara da cewa an ga motocin bas -bas suna isa kurkukun da ake tsare da falasdinawa. Sannan ana saran yahudawan zasu saki fursinoni 2000. Amma kada a manta bayan  fara yakin tufanul Aksa HKI ta kama falasdinawa fiye da 10,000 a tsakanin Gaza da yamma da kogin Jordan.

Gwamnatin HKI dai ta tabbatarwa yahudawan kasar kan cewa ba zai yu a gano ko da gawan wasu wadanda kungiyar Hamas ta kama a ranar 7 ga watan Octoba ba saboda sun lalace sun bace a cikin kasar

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted