Wani jami’in sojan Isra’ila da ya ziyarci kasar Srilanka ya gudu ya bar kasar bayan da aka sanar da shi cewa ana shirin kama shi akan laifukan yaki a Gaza.
Jaridar “Up Isra’ila” ta buga labarin cewa wata kungiya mai goyon bayan Falasdinawa a kasar Srilanka ta ja kunnen wani sojan Isra’ila akan ya fice ya bar kasar, ko kuma ya fuskanci kamu akan laifukan da ya aikata na yaki a Gaza.
Kungiyar mai goyon bayan Falasdinawa mai suna: “Hindu-Rajab” ta wallafa hoton wani sojan Isra’ila a ranar Alhamis din da ta gabata tare da cewa ta bukaci mahukuntan kasar ta Srilanka su kama shi, haka nan kuma kotun kasa da kasa ta manyan laifukan da kuma hukumar ‘yan sanda ta duniya “Interpol” saboda kashe wani farar hula da ya yi a Gaza.
Sojan na Isra’ila dai ya wallafa wani faifan bidiyo a shafinsa na “Instegram’ a ranar 9 ga watan Ogusta da a ciki ya nuna gawar wani Bafalasdine da ya kashe. An nuna shi yana yin dariya a gaban gawar wannan bafalasdinen.
Tashar Talabijin din Isra’ila ta 12: Ta ce irin haka ta faru da wani sojan ‘yan sahayoniyar a kasar Cyprus da wasu kasashe.