An Fara Aiki Da Zango Farko Na Tsagaita Wutar Yaki A Gaza

Wata majiyar Falasdinawa ta bayyana cewa bayan amincewa da kawo karshen yakin Gaza,da ake tattaunawa a Sharem-Shiekh na kasar Masar, an fara aiki da tsagaita

Wata majiyar Falasdinawa ta bayyana cewa bayan amincewa da kawo karshen yakin Gaza,da ake tattaunawa a Sharem-Shiekh na kasar Masar, an fara aiki da tsagaita wuta a hukumance.

Raidiyon HKI ya sanar da cewa, da karfe 12;00 na rana a yau Alhamis ne aka fara aiki da tsagaita wutar, don haka babu wani hari da sojojin HKI za su kai a yankin na Gaza.

Majiyar Radiyon na HKI ya kuma ce; ‘Yan aiken Amurka biyu da su ne, Steven Charles Witkoff da Jared Corey Kushner sun halarci taron na Sheram-Sheikh a yau Alhamis.

Jami’an Falasdinawa dai sun bayyana cewa aiki da wannan yarjejeniyar dai yana da alaka ne da yadda jami’an Haramtacciyar Kasar Isra’ila za su yi aiki da ita.

Su kuwa kafafen watsa labarun Masar sun bayyana cewa; Daga cikin wadanda su ka halarci taron nay au da akwai wakilan Masar, Katar, Turkiya da Amurka.

Da safiyar yau Alhamis ne dai kungiyar gwgawarmaya ta Hamas ta fitar da bayani da a ciki ta bayyana amincewa da kawo karshen yaki da kuma sakin fursunonin yaki.

Bayanin na kungiyar Hamas ya kuma ci gaba da cewa, tare da sauran kungiyoyin gwagwarmaya sun yi nazari mai zurfi akan shawarar shugaban kasar Amurka ta kawo karshen kisan kiyashin da ake yi wa Falasdinawa.

A can Amurka shugaba Donald Trump  wanda ya gabatar da jawabi akan tsagaita wutar, ya kuma bayyana cewa; A ranar Litinin ko Talata ne za a saki fursunoni.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments