An Fallasa Shirin Natanyahu Da Google Na Farfagandar Ta Dalar Amurka Miliyon $45

Kamfanin sadarwa ta Google a halin yanzu tana aiwatar da yakin farfaganda ga Natanyahu a shafukan yanar gizo da kuma dukkan kafafen da kamfanin yake

Kamfanin sadarwa ta Google a halin yanzu tana aiwatar da yakin farfaganda ga Natanyahu a shafukan yanar gizo da kuma dukkan kafafen da kamfanin yake da shi don kyautata fuskar Natanyahu da kuma HKI a duniya.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, aikin wanda Natanyahu ya sayeshi da dalar Amurka miliyon 45 zai rage irin kiyayyar da ake masa a duniya da kuma gwamnatinsa. Sannan mai yuwa ya rage irin takurawa da ake masa kan kissan kiyashin da sojojinsa suke aikatawa a gaza da kuma kasar Falasdinu da suka mamaye.

Daga karshe dai gwamnatin Natanyahu ya fake da farfaganda ta karya don wanke faska da hannayensa tare da amfani da kamfanin google don boye aiyukan ta’adanci da kissan kare dangin da yake yi a gaza, wanda ya hada da amfani da yunwa a matsayin makami a kan gaza.

Labarin ya kara fa cewa ofishin firay ministan HKI da kansa ne ya dauki nauyin farfaganda mai tsanani wanda kamfanin google ya fara yi babu kakkautawa don ganin ya wanke Natanyahu da gwamnatinsa daga aikata kissan kiyashi da kuma kare dangi, musamman saboda kissan jarirai da yunwa wanda yake yi a gaza.

Kontragin wanda ya hada da wanda kafafen yana labarai na Amurka suka fara gadan-gadan zai hana da shi Google da kuma Youtube, X, Meta da wasu, wanda zai lakume miliyoyin dalar Amurka don cimma wannan manufar.

Daga cikin farfagandar karyan da wadannan kafafen yada labarai ko na sadarwa zasu yada har da cewa “Akwai abinci a Gaza” duk wani labari banda wannan karaya ce” kamar yadda wani ministan Natanyahu ya fada, wanda kuma mutane miliyon 6 suka kalla.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments