An Dakatar Da Ayyukan Jam’iyyun Siyasa A Kasar Mali

Majalisar koli ta sojojin kasar Mali ta sanar da dakatar da ayyukan jam’iyyun siyasa da duk wasu kungiyoyi masu alaka da su. A ranar Larabar

Majalisar koli ta sojojin kasar Mali ta sanar da dakatar da ayyukan jam’iyyun siyasa da duk wasu kungiyoyi masu alaka da su.

A ranar Larabar da ta gabata ne dai majalisar sojan kasar ta Mali ta fitar da dokar wacce shugabanta janar Assimi Goita ya rattaba wa hannu, wanda kuma aka sanar ta kafafen watsa labarun kasar.

Sanarwar ta ce, an dakatar da ayyukan jam’iyyun siyasar har illa masha Allahu.

Dakatar da ayyukan jam’iyyun siyasar bai shammaci ‘yan siyasar kasar ta Mali ba, bayan da a baya a taron kasa da aka yi, aka gabatarwa da gwamnatin sojan shawarar dakatar da jam’iyyun siyasar da kuma nada shugaban majalisar koli ta sojan kasar a matsayin shugaban rikon kwarya na tsawon shekaru biyu, da kuma za a iya sabuntawa.

A karon farko, daruruwan mutanen kasar sun fito wani gangami a makon da ya shude domin yin kiran a mayar da kasar kan turbar demokradiyya.

Wani daga cikin  wadanda su ka tsara gangamin Sheikh Umar Dombiya ya fada wa kamfanin dillancin labarun AP cewa; “Ban yi mamakin wannan matakin ba, na tsammaci farwuarsa, domin wannan shi ne tunaninsu,amma za mu ci gaba da aiki tukuru domin kare tsarinmu na demokradiyya a Mali.

Masu Zanga-zangar dai sun rika bayar da taken nuni kin jinin mulkin soja.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments