A yau ne aka bude kasuwar baje koli na kayakin da suka shafi man fetur da gasa wadanda aka kera a JMI karo na 29 a yau a nan birnin Tehran.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa kasuwar zata ci ne daga yau 8-11 ga wannan watan na mayu da muke ciki.
Labarinn ya kara da cewa kamfanoni fiye da 2000 daga ciki da kuma wasu kasashen duniya 14 ne suka halarta ta. Baje kolin yana nuna matsayin JMI a fagen makamashi a duniya.