A Nijar yau ne aka bude babban taron kasar, wanda zai tsara dokoki kan yadda za’a tafiyar da kasar a lokacin mulkin rikon kwarya na soji.
Shugaban Nijar Janar Abdourahamane Tiani ne ya kaddamar da taron a Yamai babban birnin kasar inda ake sa ran shafe kwanaki hudu ana tattaunawa.
Taron zai kuma bayar da shawara kan tsawon wa’adin gwamnatin rikon kwarya.
Taron ya samu halartar tsofaffin shugabannin kasar ciki har da Mahamadou Issoufou da tsofaffin shugabannin majalisar dokokin kasar da tsofaffin firaministoci na kasar da wasu baki daga Burkina Faso da Mali da wasu kasashen.