An Bude Babban Taron Afrika Kan Matsalar Ruwan Sha A Kasar Chadi

A Yau ne bude babban taron Afrika kan matsalolin ruwan sha da kasashen yankunan ke fama da shi a kasar Chadi, taron da yana zuwa

A Yau ne bude babban taron Afrika kan matsalolin ruwan sha da kasashen yankunan ke fama da shi a kasar Chadi, taron da yana zuwa ne a dai-dai lokacin da Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce akalla mutanen Afrika miliyan 400 ne basu da ruwan sha.

Ƙididdiga ta nuna cewa akwai ƴan Afrika sama da miliyan 7 da kwata-kwata basa samun tsaftataccen ruwan sha, kuma akwai bukatar kasashen su hada kai wajen cike wannan babban gibi.

Kaso 90 na albarkatun ruwan da nahiyar Afrika ke da shi ya ratsa zuwa fiye da iyakokin rabin kasashen nahiyar, a sakamakon haka ake ganin ya kamata masu shirya taron su yi nazari kan yadda kasashen za su amfana da ruwan musamman a bangaren sha da kuma amfanin yau da kullum.

Taron ya hada da shugabannin kasashe, ministocin ruwa da na noma da kuma na makamashi, da manyan cibiyoyi da kuma hukumomin kula da rafuka da tafkuna da kuma bankuna da wasu masu zuba jari.

Yayin da yake bude taron, shugaban kasar ta Chadi Mahamat Idriss Deby ya ce baya ga batun samar da ruwan sha, nan da zuwa shekara mai zuwa kasar zata baiwa ƴan Afrika damar shiga kasar ba tare da shaidar Visa ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted