A ci gaba da nuna bacin ran da yahudawan sahayoniyya a yankunan Falasdinawa da aka mamaye suke ci gaba da yi, iyalan wadanda aka yi garkuwa da ‘yan uwansu a matsayin fursunonin yaki da masu goyon bayansu da kuma wadanda suke kin manufofin siyasar fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu da ci gaba da kasancewarsa fira minista, suna ci gaba da fitowa zanga-zangar neman kifar da gwamnatin Netanyahu, da kuma hanzarta kulla yarjejeniyar musayar fursunoni tsakanin yahudawan sahayoniyya da ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa.
Kafafen yada labaran yahudawan sahayoniyya sun watsa rahotonnin cewa: A jiya Alhamis, dubban masu zanga-zanga a birnin Tel Aviv na haramtacciyar kasar Isra’ila, sun kwarara a kan tituna, inda suka nufi hedkwatar sojojin gwamnatin mamaya, domin neman a kulla yarjejeniyar sakin fursunonin yahudawan sahayoniyya da kungiyar Hamas ta yi garkuwa da su.
Jaridar Times ta Isra’ila ta bayyana cewa: Wasu gungun masu zanga-zangar sun dauki akwatunan gawarwaki 27 na bogi, wadanda ke wakiltar fursunonin yahudawa 27 da sojojin Isra’ila suka kashe a Gaza.
Wadannan zanga-zangar dai na zuwa ne a cikin darare na biyar a jere bayan da sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suka sanar a ranar Lahadin da ta gabata cewa sun kwato gawarwakin wasu yahudawan sahayoniyya daga hannun ‘yan gwagwarmayar kungiyar Hamas da a yayin kwato su suka rasa rayukansu.