An Amince Da  Sauye-sauye A Tsarin Mulkin Kasar Benin

A kasar Benin an amince da wasu sabbin sauye-sauye a cikin tsarin Mulki wanda ya kunshi kafa majalisar dattijai da kuma tsawaita wa’adin shugabancin kasa

A kasar Benin an amince da wasu sabbin sauye-sauye a cikin tsarin Mulki wanda ya kunshi kafa majalisar dattijai da kuma tsawaita wa’adin shugabancin kasa da na ‘yan majalisu.

Sabon wa’adin da ‘yan majalisar dokokin kasar su ka amince da shi, shi ne shekaru bakwai, bayan da ya kasance shekaru biyar. Sai a shekara mai zuwa ta 2026 ne dai sabbin sauye-sauyen da aka yi za su fara aiki.

Sai dai shugaban kasar da yake ci a yanzu Patrice Talon ba zai ci moriyar wannan sauyin ba saboda watanni bakwai su ka rage wa’adinsa na biyu ya kare.

 A karkashin sauye-sauyen da aka yi, an kirkiro majalisar dattijai da za ta kasance da mambobi 25 zuwa 30. Kuma wadanda za a zaba su zama wakilai a wannan majalisar ta dattijai su ne masu kwarewa a fagen siyasa, tsaro, tsofaffin shugabannin kasa, tsoffin ‘yan majalisar dokoki, alkalai da kuma jami’an soja.

Daga cikin aikin da majalisar dattijan za ta yi da akwai karfafa hadin kan kasa, demokradiyya da zaman lafiya. Har ila yau Majalisar za ta rika yin bita ta biyu ta duk wata doka da majalisar dokoki za ta amince da ita,musamman wadanda su ka shafi harkokin kudi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments