Amurka Za Ta Fice Daga Hukumar Kare Hakkin Dan Adam Ta MDD

Shugaban kasar Amurka Donald Trump zai rattaba hannu kan wasu takardun bayar da umarni na bangaren zartaswa, game da janyewar Amurka daga hukumar kare hakkin

Shugaban kasar Amurka Donald Trump zai rattaba hannu kan wasu takardun bayar da umarni na bangaren zartaswa, game da janyewar Amurka daga hukumar kare hakkin bil’adama ta majalisar dinkin duniya (UNHRC) da kuma dakatar da bayar da tallafi ga hukumar bayar da agaji ga Falasdinu ta majalisar dinkin duniya (UNRWA).

Wata kafar yada labarai ta cikin gida a Amurka ta bayar da rahoton haka, daga wata majiya ta hukuma a fadar White House.

Yau talata kuma Trump na ganawa da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, wanda ya dade yana sukar hukumar ta bayar da agaji ga Falasdinu ta UNRWA.

A lokacin wa’adin farko na mulkin Trump a watan Yunin 2018, Amurka ta fice daga hukumar kare hakkin bil’adama ta majalisar dinkin duniya, tana mai cewa hukumar ta bayar da damar zama mamba a cikinta ga kasashen da ba su cancanta ba, kuma ta kafa kahon zuka da kuma nuna muguwar kiyayya mara iyaka ga Isra’ila. 

Tun dai bayan hawansa mulkin AMurka a karo na Biyu Trump ya sanar da soke yarjejeniyoyi da dama da kuma janye kasarsa daga wasu kungiyoyi na kasa da kasa.

Na baya baya nan ita ce hukumar lafiya ta Duniya, WHO, da kuma soke tallafin da Amurka ke baiwa kasashen ketare in ban da na kawar kasar Isra’ila da kuma Masar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments