Amurka: Turmp Yana Son Yin Yarjejeniya Ne Da Iran Ba Yaki Ba!

A bayan wata hira da tashar talabijin din, manzon musamman na Amurka a yankin gabas ta tsakiya Steve Witkoff ya rubuta a shafinsa na; X

A bayan wata hira da tashar talabijin din, manzon musamman na Amurka a yankin gabas ta tsakiya Steve Witkoff ya rubuta a shafinsa na; X cewa; Sakon da Trump ya aike wa  Tehran ba ta nufin yin barazana.

Manzon na Amurka ya riya cewa;wasikar ta kunshi cewa; Ni shugaban kasa ne mai son zaman lafiya , abinda  nake son bayyanawa kenan, don haka babu bukatar a yi magar yaki. Wajibi ne mu zauna mu tattauna.”

Wittkoff ya kuma ce; Da akwai hanyoyi na bayan fage da ake tatatunawa da Iran.

Har ila yau ya kara da cewa; Abinda Trump yake so shi ne warware sabanin da ake da shi.

Shafin watsa labaru na Axos ya bayyana cewa; Waskiyar da Trump din ya aiko wa Iran ta kunshi ayyana wa’adin watanni biyu na cimma  sabuwar yarjejeniya Nukiliya.

Wannan sabon matsayin na Amurka dai ya zo ne,bayan da mahukunta a jamhuriyar musulunci ta Iran suka bayyana cewa; Amurkan ba za ta sami wani abu daga Iran ba ta hanyar barazana.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments