Gwamnatin Washington, ta sanar da cewa nan ba da jimawa ba shugaban kasar Donald Trump da takwaransa na Rasha Vladimir Putin, zasu fara tattaunawa kan batun Ukraine da nufin tsagaita wuta don kawo karshen yakin da kasashen biyu ke yi ta hanyar tattaunawa.
Shugaban na Amurka ya sanar a ranar Laraba cewa ya yi doguwar tattaunawa da takwaransa na Rasha, kuma shugabannin biyu Shugabannin biyu sun shirya ganawa a karon farko a kasar Saudiyya.
Donald Trump da Vladimir Putin sun amince su “yi aiki tare sosai” tare da fara tattaunawa “nan da nan” kan Ukraine.
Kremlin ta tabbatar da cewa tana son “magance rikicin Ukraine ta hanyar “tattaunawar zaman lafiya”.
Tattaunawar ta wayar tarho tsakanin Donald Trump da Vladimir Putin a ranar Laraba, ta yi tasiri, a cewar washington.
Shugaban na Amurka ya bayyana cewa, “Mun amince da yin aiki tare, gami da ziyartar juna a kasashen.”
Kakakin fadar Kremlin Dmitry Peskov ya shaidawa manema labarai cewa Vladimir Putin ya shaidawa shugaban Amurka cewa yana son a samar da mafita a rikicin Ukraine ta hanyar “tattaunawar zaman lafiya.” Ta hanyar magance musabbabin rikicin,” in ji shi.
A cewar Dmitry Peskov, Vladimir Putin “ya gayyaci Donald Trump ya ziyarci Moscow kuma ya bayyana shirinsa na karbar jami’an Amurka a Rasha.” Kuma duka biyun “sun amince da ci gaba da tuntuɓar juna, gami da gudanar da taruruka.”